Rashin Ilimin Addini Ke Sanya Mata Kashe Mazajensu…. Inji Yahaya Yusuf

An bayyana rashin ilimin addini  matsayin babbar matsalar dake haifar da yawaitar kashe- kashe da mata suke yiwa mazajensu da sunan kishi lamarin da ke haifar da matsaloli a cikin harkokin sure.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Wakilin Yaki da jahilcin Zazzau, Alhaji Yahaya Yusuf Mahmud, a zantawarsa da manema labarai Jim kadan bayan kammala taron bita na azumin Ramadan Wanda aka shiryawa matan aure wanda kungiyar Umulkhairi ta shirya.

Alhaji Yahaya Yusuf, ya bayyana cewa duk matar da ta samu ilimin addini ba zata iya aikata kisa ko musgunawa majinta ko ‘ya’yan wasu ba, a cewarsa, ilimin add in I yana kara sanyawa mace tsoron Allah da sanin yadda zata kyautatawa mijinta.

Basaraken ya jawo hankalin malam an addini da suka kara dagewa wajen nunawa matan aure hanyoyin da ya kamata su kyautatawa mazajensu da kuna kara sanya musu tsoron Allah a zukatansu, ta yadda zasu kaucewa shiga cikin halin mugun kishi lamarin da ke Sanya su aikata munanan ayyukan da na sani.

Akan hakan, Wakili ya bayyana gamsuwarsa akan kokarin kungiyar Umulkhairi na shirya taron a dai dai lokacin da matsalar yawaitar kashe kashen mazaje ga matan aure da kuma musgunawa kananan yara.

Leave a comment