Gwamnatin jihar Kaduna Ta Kwato Shanu Sama Da Guda 1000  A Hannun Barayi


A kokarin da take na magance matsalar  barayi   masu satar shanu a fadin jihar, gwamnatin jihar Kaduna ta kwato shanu sama da 1000 daga hannun barayin shanu a karamar hukumar Birnin Gwari da Kachia.

Kakakin gwamnatin jihar Kaduna Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wani shirin Gidan rediyon Liberty mai suna ” Tsaro hakkin Al’umma ” inda yace gwamnati ta himmatu wajen kare rayukan al’ummar jihar baki daya.

Samuel Aruwan, yace an kwato shanu guda 900 a karamar hukumar Birnin Gwari, sai kuma guda 300 da doriya a karamar hukumar Kachia, Wanda yace yanzu haka jami’an tsaro dake  jihar Kaduna sun dukufa babu dare babu rana wajen bankado muyagun mutane musamman barayin shanu a fadin jihar.

Akan hakan, kakakin gwamnatin ya bukaci Fulani da suuran Jama’a da su taimakawa gwamnati da sahihan bayanai akan barayin shanu da sauran muyagun mutane da basu amince da su Ba Wanda hakan zai taimakawa gwamnatin.

Hakazalika, Aruwan, yace yanzu haka an samu gagarumar nasarar tsaro a kudancin jihar Kaduna da sauran sassan jihar Kaduna baki daya.

Leave a comment