Buhari Zai Dawo  Nijeriya Ranar Asabar …  Inji  Fadar Shugaban Kasa


​Rahotanni daga fadar Shugaban kasa  sun bayyana cewa, ana    sa ran  shugaban  Muhammad Buhari zai dawo gida daga birnin Landan  a ranar Asabar mai zuwa.

Idan za’a iya tunawa dai a ranar 7 ga watan Mayun da ta  gabata ne, shugaba Buhari ya tafi birnin Landan  domin duba lafiyarsa bayan ya mika ragamar mulkin kasar a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

Rahotannin sun ruwaito Uwargidan shugaban wacce  ta ziyarci mai gidanta a Landan  Hajiya A’isha Buhari ta bayyana cewa , shugaban na murmurewa cikin gaggawa kuma nan ba da jimawa ba zai dawo gida  Nijeriya.

Hajiya A’siha, tace, shugaban ya yaba da  addu’oin fatan alheri da ‘yan kasar ke yi ma sa na samun sauki inda yace yana godiya.

Hakazilika, idan ba’a manta ba a tafiyar Shugaban Buhari  ta farko da ya yi a cikin watan Janairu, shugaban ya shafe tsawon watanni biyu yana jinya a Landan, yayin da har yanzu hukumomin Najeriya ba su sanar da hakikanin rashin lafiyar da ke damun shugaban ba

Leave a comment