Mun Gamsu Da Ingancin Takin Buhari    ….Sarkin Noma


Sarkin Noman jihar Kano Alhaji Umar Yusuf, ya bayyana gamsuwarsa akan takin gwamnatin tarayya Wanda akewa lakabi da takin “Buhari” inda yace ya gamsu da ingancin takin.

Alhaji Umar, yace duk manomin da yayi amfani da takin zai tabbatar da ingancin takin, yana mai cewar ” Na sayi takin buhu guda 3000 na zuba a gonata bayan kwana uku da na koma gonar naga canji sosai yabanya tayi kyau.

Ya ci gaba da cewa” lokacin da akace gwamnatin tarayya zata fara Samar da taki ina daga cikin masu cewa wannan shiri ba zai dore ba domin duk wani shirin da gwamnati zatayi baya tabbata, amma gaskiya wannan shirin takin ya burgeni kwarai, fatan mu  shine Allah yayiwa gwamnati da wadanda aka dorawa alhakin Samar da takin jagora” inji Sarkin Noma.

A zantawarsa da manema labarai akan yadda shirin takin yake gudana, manajan kamfanin sarrafa taki na ‘MFB Fertilizer and chemicals’ Injiniya Abdu M. Kanti, ya bayar da tabbacin cewa duk wani kamfanin sarrafa taki da gwamnati ta dorawa alhakin Samar da taki suna iya bakin kokarinsu na Samar da takin mai inganci, inda yace su a kamfanin su suna Samar taki tirela 280 a kullum Wanda kuma suna aiki babu dare babu rana wajen ganin manoma sun samu takin yadda ya kamata.

Ya kara da cewa kamfanin su yana bin dokokin da kungiyar FEBSAN da gwamnatin tarayya ta tsara na Samar da takin. Yace zasu ci gaba da yin  yadda ya kamata domin Samar da takin kamar yadda aka tsara.

Leave a comment