Zamu Hukunta Masu Yiwa Takin Gwamnati Zagon Kasa ….. Inji Rabi’u Kwa

A dai dai lokacin da  sShugaban   kasa Muhammadu Buhari ya farfado kamfanonin sarrafa takin zamani a fadin kasar domin Samar da takin gwamnati Wanda za’a sayarwa manoman kasar akan farashi mai sauki, a bangare guda kuma dillalan takin sun fara yin algus a cikin takin da gwamnatin tarayya ta fara sayarwa manoma.

Dillalan takin suna sarrafa nasu takin daban Mara inganci sai su zuba shi a cikin buhun takin gwamnatin tarayya suna sayarwa da manoma akan farashin gwamnati Wanda kuma takin nasu masana kimiyya sun bayyana shi a matsayin illa ga amfanin gona da lafiyar biladama.

A jihar Kaduna jami’an tsaro na farin kaya wato (Civil Defence) sun kama buhunan taki guda 1000 a karamar hukumar Zariya da Makarfi wadanda akayiwa garwaye aka sanya su cikin buhun gwamnatin tarayya.

A kwanan baya kwamitin Samar da takin zamani Wanda shugaban kasa Buhari ya kafa, sun kawo ziyarar gani da ido a kamfanin sarrafa taki da ke jihar Kaduna domin tabbatar da cewa ana yin takin mai inganci kamar yadda gwamnatin ta umarta da ayi.

Kwamitin Wanda gwamnan jihar jigawa Alhaji Badaru Abubakar yake jagotanta sun jadda cewa duk Wanda aka kama yana sayarwa da manoma takin akan farashin Kudi sama da naira Dubu biyar da Dari biyar (5,500) ko kuma yana yin algus a cikin takin gwamnati zai fuskanci Fushun hukuma, inda yace, shugaban kasa yace a rubuta lambar Waya aka buhun takin domin kiran su idan aka samu wata Matsala

A zantawarsa da manema labarai babban sakataran kungiyar masu sarrafawa da Samar da taki ta kasa (FEBSAN) Alhaji Ahmed Rabi’u Kwa, ya bayyana cewa duk wani Wanda suka kama yana yin algus a cikin takin, zasu hukuntashi inda yace tuni aka baza jami’an tsaro da su tabbatar da sun binciko duk wani bata garin da zai kawo musu cikas akan Samar da takin.

Akan hakan Alhaji Rabi’u Kwa, ya bukaci al’ummar kasar nan musamman manoma da su tabbatar da cewa sun sanar da rahoton duk wani Wanda yake kara farashi da kuma Yiwa takin algus, inda yace  a Sanya lambar Waya akan bugun takin wanna za’a iya kira da zarar an samu Matsala akan takin.

Ya kara da cewa zasu hukunta duk masuyiwa Samar da takin zagon kasa, yana mai cewa gwamnatin tarayya ta himmatu wajen ganin an Samar da taki ga daukacin manoma kasar nan.

Rahotanni sun gano cewa yunkurin gwamnatin na Samar da taki mai inganci da saukin farashi, baiyiwa dillalan takin dadi ba musamman ganin cewa an hana su cin karensu babu babbaka akan harkar takin kamar yadda suke yi a baya.

Ya zuwa yanzu jihohin Kaduna da Gombe da Zamfara manoma sun fara fargabar sayen takin gwamnati Wanda akewa lakabi da takin “Buhari” domin tunanin fadawa hannun muyagun Dillalai.

Leave a comment