Cin Hanci Da Rashawa: Gwamnatin Kaduna Ta Kori ‘Yan KASTELEA 124

 

A kokarin ganin an magance matsalar cin hanci da rashawa a daukacin ma’aikatun gwamnati da hukumomi, Gwamnatin Jihar Kaduna ta kori ma’aikatan Kula da bin dokar hanyoyi da gyara muhalli 124 saboda saba wasu dokoki da ya hada da karban cin hanci wajen masu laifi da sauransu.

Kamar yadda shugaban hukumar KASTELEA  Kanar AbdulKadir Ahmed mai murabus, ya sanar ya ce hukumar ta sallami mutum daya saboda kama shi da ta yi dumu dumu yana karban cin hanci.

Dama dai jama’ar Jihar Kaduna sun dade suna kokawa akan yadda jami’an suke tursasa musu bayar da NA goro lamarin da ya kai ba hammata iska a lokuta da dama musamman a yankunan kawo da tudun wada.

Sauran kuma suna gujewa wajen aikinsu.

Leave a comment