Ana  Zargin  Jami’an  Gwamnati  Da Karkatar  Da Taki  A  Karamar Hukumar Birnin  Gwari

A kokarin da gwamnatin jihar kaduna kayi na Samar da taki ga Manoman jihar, Manoman karamar hukumar Birnin Gwari suna Zargin jami’an  ma’aikatan aikin gona  ta jihar da Karkatar da Takin da gwamnatin jihar ta warewa Manoman karamar hukumar.

Binciken da wakilinmu ya gudanar a karamar hukumar birnin Gwari ya tabbatar da cewa Gwamnatin ta aiki da taki  tirela Biyu a makon  da ya gabata Amma an Karkatar da takin zuwa ga ‘yan kasuwa  maimakon a bawa Manoman karamar hukumar.

Manoman birnin Gwari sunce gwamnatin jihar kaduna ta bawa Manoman karamar hukumar Taki tirela 70 wanda daga ciki an Kai musu tirela 7 wanda a makon da ya gabata an tura tirela biyu Amma baikai ga Manoman karamar hukumar ba. 

Manoman sunce duk badakalar takin da gwamnatin jihar ta warewa Manoman karamar hukumar Akwai hadin baki da manyan jami’an ma’aikatan aikin gona ta jihar da  wakilan  da ma’aikatan  sarrafa Taki ta tura karamar hukumar birnin Gwari. Akan hakan sun bukaci gwamnatin da ta tabbatar ta Binciki lamarin domin kawo  musu dauki. 

Sai dai mai Kula da dakin  da ake ajiye takin wanda kamfanin  takin ta turo a Kula da takin mai suna Malam Adamu shine Ke Karkatar da takin zuwa ga yan kasuwa maimakon a bawa Manoman karamar hukumar birnin Gwari.

Mun nemi jin ta bakin malam Adamu domin sanin halin da takin Manoman karamar hukumar  yake,  inda yace shi ” banda masaniyar komai Akan takin saboda Ni Babu hannu Na a ciki” Inji shi. 

Da yawan  Manoman karamar hukumar birnin Gwari sun  sayi  takin Kuma sun bada kudinsu  Amma ba’a basu takin ba har ya zuwa yanzu Babu labarin takin inda Suka ce duk manomin da ya biya kudin  takin basa samu. Binciken mu ya tabbatar da cewa takin da gwamnatin jihar ta warewa Manoman karamar hukumar birnin Gwari Ana sayar  da shi  a kasuwa.

Mun nemi jin ta bakin maaikatar aikin gona ta jihar kaduna domin jin ta bakin su, inda daraktan  aikin gona ta ma’aikatan  mista  Bege, inda yace Shima ya samu labarin  hakan Yana mai cewa Babu shakka sun tura tirela biyu Amma  Ance bai Kai ga Manoman ba yace Zai bincika lamarin. 

Manoman karamar hukumar birnin Gwari suna Kira ga gwamnan jihar kaduna da taimaka musu wajen ganin yakawo  musu gudummawa domin tabbatar da cewa an kawo musu takin da Suka biya kudinsu. 

Leave a comment