An  Karrama Kamfanin Aikin Hanya Na GULU Da Lambar Yabo 

A bisa kokarin da kamfanin aikin hanya na “Gulu   Engineering”  da Ke jihar Kano yake gudanarwa wajen gina  ingantattun hanyoyi  a fadin Kasar nan musamman a Arewacin NIjeriya, kungiyar ‘yan jarida sun karrama kamfanin aikin hanya na GULU engineering da lambar yabo a matsayin kamfanin aikin hanya mafi shahara a Arewacin NIjeriya.

Kamfanin GULU wadanda suna daga cikin kamfanonin aikin hanya da suke aiki a jihar kaduna wanda Kuma suna daga cikin kamfanonin mafi aiwatar da aikin hanya mafi ingancia jihar. 

Binciken da wakilinmu ya gudanar a jihar kaduna ya bayyana cewa Gwamnatin jihar tana alfahari da aikin kamfanin GULU wanda ya taso daga Babban filin tashin Jiragen Sama da  Ke kaduna ya wuce zuwa unguwar  Rigasa dake cikin karamar hukumar Igabi  a jihar kaduna. Aikin hanyar wanda ya samu gagarumar yabo daga wurin jama’ar jihar dama masu wucewa ta jihar kaduna.

Aikin Hanyar Yana daga cikin aikin da kungiyar ‘yan jaridar Sukayi  La’akari shi wajen  bawa kamfanin lambar yabo na shekara 2017.

Da yake amsar Labar yabon a madadin kamfanin  Injiniya Mahmud Zubair, ya bayyana cewa zasu Kara ci gaba da gudanar da aiki mai inganci  a duk inda Suka samu wani aiki a fadin Kasar nan.

Inginiya Zubair wanda shine ya jagoraci aikin da kamfanin ya gudanar wanda Kai ga Suka samu lambar yabon,  ya Kuma bayar da tabbacin cewa kamfanin GULU a shirye suke da bawa Gwamnatin jihar kaduna duk wata gudummawar da ya kamata wajen ganin ta ciyar da  jihar gaba. 

Yace kamfanin GULU sun tanadi  kayan aiki irin Na zamani  wanda duk wani kamfanin aikin hanya zaiyi alfahari da su. Akan hakan ya jinjinawa kungiyar ‘yan jaridar bisa karramasu fa Suka yi  a matsayin kamfanin aikin hanya mafi shahara daga cikin kamfanonin aikin hanya.

Leave a comment