Idan Hameed  Ali Ya Magance Matsalar Fasa Kwawri, To Ya Sa Irin Kayan Da Yake So… Inji Saraki

Shugaban kwamitin da ke kula da harkar shigo da kaya Nijeriya na Majalisar Dattawa Sanata Hope Uzodinma, ya koka da yadda ake shigo da kayayyaki ta barauniyar hanya cikin Nijeriya.

Majalisar dattawa, ta ce Bankin Duniya ya bayyana cewa kayan da ake fasa-kaurin su a Najeriya sun haura Tiriliyan 7 a kowace shekara, wanda ya zarce kasafin kudin ta.

Shugaban majalisar dattawa Abubakar  Bukola Saraki, ya ce idan har ana so a magance matsalolin tattalin arzikin dole a shawo kan wannan matsala.

Rahotanni dai sun ruwaito   Saraki ya na cewa, muddin Kanar Hamid Ali ya yi maganin matsalar fasa-kauri a Nijeriya, to ya sa duk tufafin da ya ga dama, kuma zai mara masa baya a kan wannan kudiri.

Leave a comment