Kungiyar masu sayar da magunguna ta kasa (NAPPMED) reshen jihar Kano ta bayyana kudirinta na tallafawa gwamnatin jihar Na kawo karshen Matsalar masu sayar da muyagun kwayoyi a fadin jihar.
Kungiyar tace A shirye take Da ta Magance Matsalar yawaitar masu sayar da magungunan Maye a jihar Kano wanda hakan Yana daga cikin abubuwan da kungiyar ta sanya a gaba.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Malam Dahiru Abdullahi Matazu, wanda shine uban kungiyar masu sayar da magunguna ta jihar kano, (NAPPMED) yace “Muna bakin kokarinmu na kawo karshen Matsalar masu shaye-shayen muyagun kwayoyi wadanda ake sayar da su a shaguna.
Ya Kara da cewa yanzu Haka kunhiyarsu ta kafa wani kwamiti da Zai rinka Shiga shaguna suna duba irin magungunan da ake sayarwa da zimmar bankado masu sayar da muyagun kwayoyi a kasuwar sabon gari. Acewarsa tuni wannan kwamitin ya Fara kama irin wadannan masu shagunan Kuma suna karbar magungunan.
Yace baya ga kama masu sayar da muyagun kwayoyi suna kwato magungunan da basu da inganci wadanda ake sayarwa jama’ar jihar, inda yace Idan sun kama irin wadannan magungunan suna Mika su ga jami’an tsaro wasun su Kuma su rabawa masu cutar amosanin jini (sicle cell) kyauta.
Malam Dahiru, ya ci gaba da cewa “Muna so mu bawa Gwamnatin jihar Kano goyon baya domin ganin an Magance Matsalar yawaitar masu shaye- shaye.
“Muna bukatar gwamnatin jihar Kano data hada hannu da malaman addini da kungiyarmu wajen Magance Matsalar, saboda Haka mu a shirye muke muyi aiki da Gwamnati”inji Matazu.
Duk wanda baya sayar da magani a kasuwa sabon gari to baya tare da mu saboda Haka duk wanda Ke sayar da magani a kasuwar sabon gari shine mamban mu” a cewarsa