Matasan APC Sunyi Yunkurin  Kashe Shehu Sani, Hukunyi Da Isa Ashiru 

Wasu gungun matasan Jam’iyyar APC ya jihar kaduna sunyi Yunkurin Hakika jiga-jigan Jam’iyyar APC Akida a sakatariyar kungiyar ‘yan jaridar Na jihar kaduna yayin da suke gudanar da taron manema labarai Akan batutuwan da Suka Shafi ci gaban Jam’iyyar a jihar kaduna. 

Matasan sun shigo sakatariyar ‘yan jarida Na jihar  NUJ dauke  da makamai inda Suka nufi Kan babban tebur wanda  manyan suke Zaune


Shigowar matasan Ke da wuta sai  Suka Fara Kai musu Duka da makamai lamarin da yakai Hatta ‘yan jarida matasan sun raunata.

Wadanda matasan Suka yi Yunkurin halakawa sun hada da Sanata Shehu sani, Sanata Suleiman Hunkuyi da Isa Ashiru da dai Sauran manyan Jam’iyyar. 

Wakilinmu ya ga Shehu sani ya hauro ta katanka wanda shine matasan suke Nema Ruwa a jallo, sai dai  duk da cewa Akwai jami’an tsaro na ‘yan sanda Amma basu Hana matasan shigowa  wurin taron ba. 

Hatta ‘yan jarida  matasan sun raunata su wasun Kuma an lalata musu kayan aiki, lamarin da ya Kai ga ‘yan jarida sune Suka Kora matasan a guje. 

Leave a comment