ZABEN 2019: Talakan  Nijeriya  Ya Shirya Korar Jam’iyyar APC Daga Mulki …. Inji Makarfi 

Shugaban jam’iyyar PDP Sanata Ahmed Makarfi, ya ce talakan Nijeriya ya shirya domin korar yunwa da fatara a shekara ta 2019.

Makarfi ya bayyana haka ne a babbar helkwatar jam’iyyar da ke a Abuja, yayin da shugabannin mata na jam’iyyar PDP su ka kai masa ziyara a ofishin sa.

Sanatan ya ce, idan an lura, an jefa kasar nan a cikin yunwa da fatara wanda duk sun fi shafar talaka, ya na mai cewa sun tabbatar da talaka a shirye ya ke ya fatattaki APC a zabe mai zuwa.

Makarfi ya cigaba da cewa, babban taron da jam’iyyar za ta yi ranar 12 ga watan Agusta, zai nuna wa duniya karfin jam’iyyar, kuma PDP za ta sasanta da dukkan ‘ya’yan ta, sannan ta nemi wasu mutane na daban.

Leave a comment