Wa’adin Da Muka Bawa Inyamurai Na Barin Arewa Yana Nan Daram …. inji Matasan Arewa

Kungiyar tuntuba ta matasan Arewacin NIjeriya ta bayar da tabbacin cewa wa’adin da ta ba Inyamurai na barin arewacin Nijeriya Yana nan daram.

Matasan  sun ce, wadanda duk ke da ra’ayin kasancewa a cikin Nijeriya su na iya ci-gaba da zama a yankin arewa, amma wadanda ba su da ra’ayi su bar yankin kafin wa’adin da aka diba masu ya cika.

Shugaban kungiyar Shettima Yarima, ya ce kungiyar su ta na da burin ganin zaman lafiya ya tabbata a tsakanin al’ummomin Nijeriya inda basu da manufar kawo tashin hankali a Kasar nan baki daya.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa za su cigaba da neman shawarar Arewa maso tsakiya da Arewa maso gabas idan za su canja matsayar su.

Leave a comment