Maniyyatan jihar Katsina Sun Gudanar Da Zanga-Zanga 

A jihar katsina maniyyatan  jihar sun gudanar da wata zanga -zangar nuna rashin jin dadinka Akan yadda hukumar Kula da jin dadin alhazai take yiwa maniyyatan  jihar musamman wajen tsaikon da Jigilar alhazai da ake samu.

 Sai Kuma Shugaban hukumar kula da jin dadin alhazan na jihar Katsina Muhammad Abu Rimi, ya ce wasu ‘yan adawa sun zuga alhazan jihar su gudanar da zanga-zanga sakamakon matsalar jinkiri da aka samu wajen jigilar mahajjatan.

Abu Rimi, ya ce jam’iyyar PDP ce kan gaba wajen yada farfagandar da ta haddasa zanga-zanga da alhazan suka gudanar a jihar.

Jam’iyyar PDP ta jihar ta bayyana cewa jinkiri da aka samu ya wahalar da alhazan, wanda hakan yasa suka kwana a tashar jiragen sama.

Ata bakin Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina, Salisu Majigiri, ya zargi gwamnatin APC ta kasa tsara jigilar mahajatta yadda ya kamata, wanda a cewar sa hakan ya nuna karara cewa sun gaza a jihar.

A halin yanzu, mahajjata 2,086 daga cikin 4,000 ne suka sami tafiya zuwa kasa mai tsarki a jirgi na biyar da ya tashi zuwa kasa mai tsarki.

Leave a comment