Kungiyar Akantocin  Nijeriya Ta  Jinjinawa Gwamnatin Kaduna Akan Zaman lafiya 

Kungiyar  Akantoci ta Nijeriya  wato “Association Of National Accountants  Of Nigeria”  (ANAN)  ta bayyana gansuwarta dangane da yadda aka samu Zaman lafiya a jihar Kaduna  musamman ma a kudancin kaduna wanda hakan Zai taimaka wajen fadada  harkokin kasuwanci a fadin jihar.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar na kasa Alhaji Shehu Usman Ladan,  Inda  yace  “Gwamnatin jihar kadun tayi kokari wajen Samar da Zaman lafiya a kudancin kaduna”

Alhaji Shehu Usman Ladan,  ya Kara da cewa, Jihar kaduna tana daga cikin jihohin da Suka Fara aiwatar da asusun bai daya na Tara kudadan harajia a  fadin Kasar nan baki daya wanda hakan ya taimaka wajen rage alumdahana  da kudadan jihar.

Shugaban ya bayyana haka ne a taron kingiyar Na kasa wanda ya gudana a jihar kaduna, inda yace Gwamnatocin  Kasar nan suna kokari matuka wajen Samawa matasan ayyukan da zasu dogara da kansu duk da cewa Akwai matsalolin tattalin arziki Amma suna bakin kokarinsu.

“Duk wanda ya shigo cikin jihar kaduna Zai tabbatar da cewa Gwamnatin jihar tana bakin kokarinta na bunkasa ci gaban jihar ta fannoni da dama, saboda Haka kungiyar ANAN ta jinjinawa Gwamnatin kaduna karkashin Jagoranci malam Nasiru El-rufai”inji shi. 

Yace ” sai da Zaman lafiya za’a samu bunkasar tattalin arziki, hasalima,  babu jihar da take ci gaba muddin Babu Zaman lafiya Saboda Haka kingiyar ANAN ta jinjinawa gwamnatin jihar kaduna Akan batun Samar da Zaman lafiya a fadin jihar baki daya”

Hakazalika,  a cewarsa, gwamnan jihar kaduna El-rufai ya taka rawar gani wajen Kara bunkasa hanyoyin samun haraji  a jihar wanda hakan Zai bawa Gwamnatin damar aiwatar da ayyukan ci gaban jihar kaduna.

A nasa jawabin, gwamnan jihar kaduna Nasiru El-rufai, ya bayyana cewa Gwamnatin jihar kaduna ta dauki matakan Magance Matsalar sace kudadan jihar ta hanyar   Samar da asusun bai daya na Tara kudadan haraji.

Gwamnan wanda kwamishinan ma’aikatan kudi Alhaji Suleiman Abdu  kwari, ya wakilta, yace kudadan haraji da ake samu a jihar sun karu matuka Inda yace yanzu jihar kaduna ta  Samar da yayi mai kyau domin zuba jari. Yace jihar kaduna an samu ci gaba da Zahiri wanda shine Karo Na farko a tarihin jihar.

Taron ba kingiyar Na Bana ya samu halarcin Akantocin Nijeriya daga jihohi 36 da birnin tarayya Abuja.

Leave a comment