Yadda Hunkuyi Ya Maida Kansa Allan Siyasar Jihar Kaduna

Daga Abdul Tonga 

Na jima Ina kaucewa yin rubutu na kushe ko martani ga Sanata mai ci a yanzu, Sanata Suleiman Usman Hunkuyi. Ba domin komai ba sai saboda halakarsa da mai girma Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-rufai wanda halakace ba ta siyasa bace kawai ana iya cewa halakace ta jini.

Ga ire iren mu da muke da kusanci da iyalan Mai Girma Gwamnan, muna sane da irin halakar dake tsakanin mai Girma Gwamnan da babban wan Sule Hunkuyi wato Idris Usman Hunkuyi wanda iyalan Malam Nasir harma da shi kansa sukewa lakabi da suna Uncle Idi.

 A irin karar da muke dashi, duk wanda ya taba Sule tamkar yaci mutunci yayansa Idris ne haka kuwa duk wanda ya taba mutuncin Idi babu shakka ya taba mutuncin Mai Girma Gwamnan Malam Nasiru ne mu kuwa duk wanda ya taba mutuncin Malam ko shi wanene zamu daura zare dashi har sai yadda hali yayi. To da wannan ne na jima ina kauda kai daga bita da kullin da Sule yake daurawa Malam na butulci tun yana yi a boye har sai da ya fito fili karara ya nunawa duniya, ganin yadda yanzu ya shafawa idanuwansa fodar rashin kara da sanin ya kamata, naga lokaci yayi da zamu ankarar da shi dama masu tunanin cewa Sule na yiwa Mai Girma Gwamna alfarma ne a siyasa ba tare da sanin cewa Sule baya ga kanine a wajen Malam Nasiru haka nan ma yaronsa ne a siyasance.

Babu bukatar na koma baya na bayyanawa masu karatu irin butulcin da Sanatan Zone 2 yayi a siyasance wanda duk dalibai na siyasa da kuma masu nazarin harkar Siyasan jihar Kaduna sun tabbatar da cewa ire iren wannan butulcin da yayi a baya yayi matukar taba tasirinsa a siyasance.

Sai dai kuma a wannan karon ba sai na rantsai ba duk mutumin dayasan irin alfarma, taimako, yarda da kuma amanar da Malam ya baiwa Sule kuma ya Kirkiro fada da gangar Kawai domin ya cimma wasu mugayen manufofinsa, tabbas Karshen tasirinsa a siyasa ne yazo, domin babu inda Allah Ya bada damar cin amana ko karya alkawari da aka damkawa mutum.

Babban matsalar da Hunkuyi yake dashi shine na ganin kansa tamkar wani allah ne a siyasar jihar Kaduna, dauka yake duk wani dan siyasar da bai halakanta kansa dashi ba bazai yi tasiri ba. Hunkuyi a dauki izza na Allah Ya daurawa kansa na shiyake bada mulki a jihar Kaduna inda ya manta da yadda dare daya ya butulcewa amininsa kuma ubangidansa Ahmed Makarfi wanda ya amince masa ya bashi karfi fiye da matsayinsa na kwamishinan kudi a wannan lokacin har wasu na masa lakabi da suna “Kafi Gwamna”.

Sai dai kuma tusu na butulcin da yayiwa Makarfi na neman kujeran Gwamna a wannan lokacin yasa Allah Ya hanashi yin nasara akan Makarfi duk kuwa da yadda a wannan zamanin al’umar jihar Kaduna suka kosa da gwamanti PDP. Tun daga wannan lokacin Hunkuyi Ya disashe a siyasance sai bayan da Malam ya kawo shi a tafiyarsa ya kuma bashi Daraktan kamfen dinsa na Gwamna. Domin tun bayan da Gwamna Makarfi ya kwadashi da kasa, yayi takarkaru, ya kuma sauya shekoki na siyasa da dama amma bai yi nasara ba saboda babu wani mai jefa kuri’a da ya mallaki hankalin sa a jihar Kaduna dayake da yarda da Sule. 

Mutane da dama basu da masaniyar cewa Hunkuyi bashi da wani ubangida a siyasance da ya wuce Malam Nasir domin duk wani takara da hauma hauma da yake yi a siyasance Malam ne ke bashi kudi. Saboda halakarsu da nayi bayani a baya. Da wannan ne kuma yasa Malam ya amince masa harma yayi amfani da abunda ake Kira structure a trance na Siyasan Sanata Hunkuyi yayi yakin neman zabensa ba tare da wani tararrabi ba duk kuwa da irin jan hankalinsa da wasu da dama sukayi.

Wadanda basu bin harkar Siyasan jiyar Kaduna basu da masaniyar cewa kashi 60 cikin 100 na kwamishinonin jihar Kaduna yaran Sule Hunkuyi ne na siyasa ciki har da kaninsa uwa daya Uba daya. 

A lokacin da za a nada kantomomi na kananan hukumomi yaran Hunkuyi har yanzu sune suka dauki kaso mafi tsoka. Duk wani hidima na ciki da wajen gwamanti babu wanda mai girma Gwamnan baya tuntubar Sanata akansa. Haka zalika al’amuran siyasar jiyar sai an nemi shawararsa.

Haka kuma sai yadda Sule yake so akayi a lokacin da ake yakin neman zabe a matsayinsa da Darakta kamfen duk kuwa da irin kurakuren da yayi ta tafkawa a lokacin.

Jama’a da dama basu da masaniyar cewa gaba da bakin cikin da Sanata Shehu Sani yake yiwa Malam Nasir duk a sanadiyar Hunkuyi ne. 

Wannan damar ne da Hunkuyi ya samu, yasa ya dauka zai yi amfani da wakilansa na delegates ya nada kansa gwamna a zabe mai zuwa, sai ya manta kifin da yake da wayo a kullin idanuwansa na kallon mai jar koma ne, hakan ya fusatashi ya kasa boye butulcin da yake shirin tafkawa inda ya fake da zaben delegates.

Yana da kyau masu karatu su fahimci cewa babu wani laifi na zahiri da Mai Girma Gwamna Nasiru yayiwa Sanata har zai fito karara ya nemi muzantashi a bainar jama’a idan muka yi la’akari da halakarsu na jini da na siyasa ba dai-dai bane matakin da Hunkuyi ya dauka a yanzu na fito na fito da mai Girma Gwamna. Yana da kyau Sule ya sani babu abunda butulci kowani iri yake haifarwa sai kaskanci da zubar da mutunci ga mai yinsu. Sule ya sani da zai iya baiwa wani mulki da tuni ya baiwa kansa tunda babu abunda Hunkuyi yake sha’awa a duniyan nan irin yaga kansa a gidan Sir Kashim a matsayin Gwamna mai cikenken iko. Yana da kyau Mai Girma Sanata ya sani rashin biyayya, cin amana, butulci shiga hurumin Allah kaskanci suke haifarwa ga mai yinsu. Hunkuyi ya sani lokacin kwacen akwati ya wuce ko amfani da tarin ‘yan daba, yanzu al’umar gari ne suke zabe don haka tinkaho da tarin magoya bayan da suka Kwarai wajen satar akwati ba a wannan zamanin ba. Ina kira ga Mai Girma Sanata da kada ka bari zuciyarka ta sake fadawa tarkon shedan na kitsama butulci ga dan uwanka domin bazaka samu nasara ba ganin a bayama baka samu ba. 

Allah Ya karawa Malam Nasir lafiya da hikimar jagoranci. Allah Ya tona asirin duk masu niyar masa butulci ko cin amana.

Leave a comment