Bishop Idowu Fearon  Shi Zai Jagoranci Hukumar Zaman Lafiya A Kaduna


Gwamnatin jihar  kaduna ta bayyana sunan Shugaban Cocin darikar Anglican Bishop Josiah Idowu Fearon, a matsayin wanda zai jagoranci hukumar Samar da zaman lafiya Wanda gwamnatin ta kafa.

Gwamnan jihar Kaduna  Malam Nasiru Ahmed El-Rufai, shi ya sanar da hakan inda yace Bishop Fearon da mutane uku sune Zasu jagoranci hukumar.

Gwamna El-Rufa’i, Wanda ya bayyana hakan ta hannun Mai taimaka masa na musamman a harkokin yada labarai Samuel Aruwan, yace tuni gwamnan ya tura sunayen mutanan da zasuyi aiki hukumar ga majalisar dokokin jihar domin tabbatar da su.

Samuel Aruwan, Yace, Bishop Idowu Fearon shine shugaban hukumar sai Priscilla Yachat Anku a matsayin mataimakiya sai Dakta Saleh Bashayi Momale matsayin babban daraktan hukumar sai kuma HAJIYA Khadija Hawaja Gambo. 

Idan ba’a manta ba, A Kwanan bayane majalisar dokokin jihar Kaduna ta tabbatar da kudirin dokar kafa hukumar Samar da zaman lafiya a jihar kaduna da zimmar kawo zaman lafiya a fadin jihar baki daya.


Aruwan, ya Kara da cewa  gwamnatin jihar kaduna ta himmatu wajen ganin  an samu zaman lafiya a jihar Wanda hakan yana daga cikin manufofin gwamnatin su Yana Mai created “gwamnatin jihar bazata aminta da masu son bata kokarin su na wargaza zaman lafiya a jihar ba.

Shugaban  hukumar da mambobin sa guda uku, bincike ya nuna cewa duk sun kware wajen samar da zaman lafiya a nahiyar Afrika da gida Nijeriya wandanda kuma duk sun taka rawar gani wajen magance matsalar rashin zaman lafiy a kasashe da dama. 

Burin gwamnatin jihar kaduna shine a samu hadin kan daukacin alummar jihar baki daya domin kawo ci gaban jihar kaduna. 

Leave a comment