JITA-JITA: EL-Rufa’i Ya Karyata Zancen Tsige Mataimakinsa


Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, ya karyata rahotannin da ke cewa ya na shirin tsige mataimakin sa Barnabas Bala Bantex, tare da maye gurbin sa da tsohon sakataren gwamnatim jihar Alhaji Lawal Yakawada.

El-Rufa’i ya karyata jita-jitar ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa ta fuskar yada labarai da hulda da jama’a Samuel Aruwan ya fitar.

Ya ce labarin ba ya da tushe balle makama, wasu ne kawai masu son tada zaune tsaye, da bukatar haddasa rarrabuwar kawuna ke yada wannan jita-jita.

Gwamnan, ya kuma bukaci al’ummomin jihar Kaduna su daina daukar irin wadannan maganganu da muhimmanci, ganin cewa za su iya janyo koma baya ga jihar da ma Nijeriya baki daya.

Leave a comment