Aikin Hakar Man Fetur A  Jihar Sakkwato Yayi Nisa

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPC, ya  bayyana cewa ya zuwa yanzu aiki ya yi nisa a yunkurin nemowa da kuma hako man fetur da iskar gas a jihar Sokoto.
Hakan yazo ne a dai  dai lokacin  da gwamnatin tarayya da jihohi musamman na arewa ke kukan matsalar tabarbarewar tattalin arziki da karancin kudaden shiga.

Rahotanni sun ruwaito cewa yankunan da aka fara gano man fetur a jihar Sakkwato kuwa sun hada da Gada, da Goronyo, da Illela, da Gudu, da kuma Tangaza.

Bayanin ya fito fili ne bayan ganawar da gwamnan jihar Sakkwato ya yi da shugaban kamafanin NNPC a Abuja.

Leave a comment