FASA KWAWRIN MAKAMAI: Dalilin Da Ya Sa Muka Kori Kwastam 28 Daga Aiki….Hamid ALI


Shugaban hukumar  fasa kwawri ta kasa Kanar Hamid Ali, ya  bayyana dalilan da ya sanya suka kori jami’an hukumar 28 bisa Kama su da hannu cikin fasa kwawrin makamai,

Kanar Hamid Ali yace  bayan kammala bincike da hukumar sa ke da alhakin yi a kan lamarin, ta mika makaman da wadanda ake tuhuma ga hukumar tsaro ta farin kaya, kuma tuni an mika su ga kotu domin a yi masu hukuncin da ya dace. Hamid Ali, ya ce su kuma na su jami’an da su ka kama da hannu a cikin lamarin tuni sun kore su daga aiki.

A baya-bayan nan dai, hukumar kwastam ta Nijeriya ta kama bindigogi 470 a tashar jiragen ruwan Tincan Island a Lagos, wadanda aka shigo da su daga kasar Turkiyya, makonni kadan da kama wasu fiye da 1,000 da su ma aka shigo da su daga kasar Turkiyya.
 
Gwamnatin tarayya dai ta ce, dole ta hau teburin tattaunawa da ofishin jakadancin Turkiyya da ke Nijeriya.
 

Leave a comment