RUFDA CIKI DA DUKIYAR KASA: Za’a Binciki Hukumar JAMB 


Ministar Kudi Kemi Adeosun, ta bayar da shawarar da a gudanar da Bincike a hukumar shirya jarabawar shiga jami’a JAMB bisa zarginta sama da fadin wasu kudade.

Rahotanni sun nuna cewa, hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami’a ta JAMB, ta samu tsabar kudi sama da Naira bilyan 30 da miliyan 726 a cikin shekaru 5, amma Naira milyan 15 kawai ta sanya a asusun Gwamnatin Tarayya.Kudaden dai sun fito daga hannun daliban da su ka yi rajistar rubuta jarawabar JAMB din a tsakanin shekara ta 2011 zuwa ta 2015.

Dalibai sama da milyan 7 da su ka rubuta jarabawar a cikin shekaru 5, sun biya kudade daga Naira 4000 zuwa Nnaira 4,600 a kan kowace jarabawa.

A dalilin haka ne, Gwamnatin Tarayya ta bada umurnin a gudanar da bincike a kan shuwagabanin hukumar guda 2 da su ka shude, dangane da rashin biyan kudaden da su ka dace su biya Gwamnatin Tarayya.

Ministar Kudi Kemi Adeosun ne ta bada sanarwar binciken da za a fara gudanarwa a kan hukumar ta JAMB.

Leave a comment