Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sako Uwargidar Mai Taimakwa Gwamna Masari 


Masu Garkuwa da mutane sun sako uwargidar mai taimakawa gwamnan jihar katsina akan harkokin gwamnati dakta Lawal Bagiwa.
A wani Rahoto da kafar Labari ta Katsina Post ta wallafa tace  matar mai bai wa Gwamna Masari shawara a kan harkokin gwamnatoci Dakta Lawal Bagiwa ta kubuta daga hannun masu Garkuwa da mutanan sai dai basu bayyana nawa aka biya a matsayin kudin fansa ba.

Babban mai taimaka wa Gwamnan a kan kafafen sadarwar zamani Alh Abdulhadi Ahmad Bawa shi ne ya wallafa kubutar matar . sai dai bai bayyana yadda matar ta kubuta ba, wajen sai da aka bayar da kudin fansa ko a’a.

Allah cikin ikon Shi da buwayarShi Ya kubutar da Hajiya Binta Bagiwa ( Matar Dakta Lawal Bugiwa) daga hannun wadanda suka yi garkuwa da ita.

A ranar Talata ne dai aka samu rahoton cewa masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da uwargidan mai bai wa Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina shawara a kan harkokin da suka shafi gwamnatocin jiha da jiha Dakta Lawal Bagiwa.

Leave a comment