Sama Da Shekara 10 Ba A Samu Rikici Tsakanin Manoma Da Makiyaya A Jihar Yobe…. Inji Gaidam

 

Manajan shirye-shirye na Gandun dabbobin jihar Yobe Dakta Mustapha Gaidam, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sayi alluran rigakafi na sama da naira milyan daya da dubu dari hudu don yiwa dabbobi alluran rigakafi.

Gaidam, a hirar sa da manema labarai a kaduna yace,”a jhar Yobe muna da dabbobi domin mu a jihar  babu gidan da ba a kiwo, gidaje kashi tamanin zuwa tas’in zaka tarar suna yin kiwo.”

“Bugu da kari, a yanzu a Najeriya kidayar da aka yi na shekarar 1991 kabilun mu duka sun tabbatar cewar jihar yobe itace tafii ko wacce jiha duk kasar nan wajen dabbobi.


Ya kara da cewa, Maaikatar Noma ta tarraya ta bada kusan  9. 7  yanzu na yawan dabbobin da Yobe keda su a halin yanzu.

Yace” wamnati na taimakawa masu kiwon magunguna kyauta muke basu allura kyauta gwamnati ta sayi allurai na sama da milyan biyu.

Akan rikicin manoma da makiyaya kuwa, Gaidam yace, “mu a jihar Yobe, yau s ama da shekara goma bamu samu inda manoma da makiyaya suka yi rikici ba, dalili shine, gwamnati musamman ta Gwamna Ibrahim Gaidan ta samar da burtali ga makiyayan dake jihar Wanda hakan ya taimaka wajen magance matsalar.

Leave a comment