An Ceto Sama Da Mutane 500 Yayin Da Ake  Yunkurin  Tsallakar Da Su Nahiyar  Turai

Jami’an tsaro sun kama wasau mutane 40 inda kuma suka ceto sama da mutane 500 bayan yunkurin tsallakar da su nahiyar Turai da aka yi daga Afrika ta yamma.

Hakan na zuwa ne kolacin da duniya ke tsaka da kukan hoton bidiyon da ke yawo a kafafan internet na cinikin bayi da akayi a kasar Libya, sai dai duk da hakan mutane na ci gaba da yunkurin tsallakawa nahiyar turan.

Kungiyar ‘yan sandan kasa-da-kasa tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro ne suka sanarda hakan a jiya.

Sanarwar ta ce, yan sandan sun ceto mutane 500 wanda suka hadar da kananan yara 236, yayin sumamen hadin gwiwar da suka gudanar a yankin kasashen Chadi da Mali da Murtaniya da Niger da kuma Senegal.

Kamar yadda yake a cikin sanarwar, za’a gurfanar da mutane 40 din da aka kama da laifin safarar mutane, da tursasa kananan yara wajen aikatau.

Za’a kuma gurfanar da su kan tursasa kananan yara suyi bara da kuma karuwanci batare da mutunta hakkin dan adam ba.

Leave a comment