NOMAN SHINKAFA: Jihar Kebbi Ta Ciri Tuta

Yau kimanin shekara biyu kenan da  Shugaban kasa  Muhammad Buhari,  kaddamar da shirin noman shinkafa da alkama da kuma waken suya na rani da damina, inda shugaban ya samu rakiyar Ministan Aikin Gona, Audu Ogbeh, Gwamna Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, shugaban kungiyar manoman alkama a Nijeriya, Gwamononin Sokoto, Zamfara, Katsina, Neja, Ebonyi, Adamawa da sauran manyan jami’an Gwamnati.

Shirin da shugaban ya kaddamar, hadin gwiwa ne tsakanin Babban Bankin Nijeriya (CBN), watau (ANCHOR Borrowers), bakin bayar da tallafin noma da kuma gwamnatin jihar ta Kebbi don samar da aikin yi ga matasan kasar nan da kuma rage zaman kashe wanda ga marasa aikin yi a kasar nan.

Gwamnatin jihar, ta fito da wannan shirin ne domin ta farfado da tattalin arzikin da ke cikin noma a kasar nan, musamman bisa la’akari da tabarbarewar tattalin arzikin, ba ta hanyar dogaro da arzikin danyen man fetur kadai ba.

Saboda haka Gwamnatin Jihar, a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta ga cewa ya zama wajibi ta fito da wannan tsarin noma domin maido da arzikin noma a jahohin kasar Nijeriya. Daga nan kuma ta bukaci babban Bankin Nijeriya CBN cewa ya shigo cikin wannan shirin don bayar da tasu gudunmuwa ta hanyar bayar da tallafin kudi da kayan noman ga manoman Jihar.

Irin amfani da ci gaban da aka samu a kan noman shinkafa, alkama da kuma waken suya a jihar, shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya nada Gwamnan jihar ta Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu a matsayin shugaban kwamitin gudanar da harakar noman shinkafa da alkama a Nijeriya. Wanda a halin yanzu kwamitin sa ya ziyarci jahohin da ke noman shinkafa da alkama domin ganin irin yadda za su iya ba da tallafi ga jahohin don kara bunkasa aikin noma a kasar Nijeriya, wanda a cewar sa “burina shi ne na ga ana sayar da shinkafar Kebbi a gidajen cin abinci a New York da Japan”.

A bisa gudunmawa da kokarin gwamnan jihar, yanzu jihar Kebbi ba a maganar mutun nawa ne ke noma a jihar ba, domin kuwa kusan kashi tamanin da bakwai na mutanen jihar sun koma gona wurin noman shinkafa, alkama da kuma waken suya, domin Allah ya albarkaci jihar da mutanenta da wuraren noman shinkafa, alkama, waken suya, albasa, tumatur, wake, gero da kuma rogo da sauran su.
A shekarar 2015 ne Gwamnatin jihar Kebbi ta fito da shirin tallafin Noman shinkafa, alkama da kuma waken suya ga manoman jihar, inda aka kudurta za a samar da shinkafa da za ta iya ciyar da mutanen kasar nan wanda adadinta ya kai tan miliyan daya, karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu; cikin nasara. A shekarar 2016, jihar Kebbi ta samar da shinkafa da ta zarce tan miliyan daya da rabi.
Daga cikin nasararon da harkar noma ta samar wa jihar Kebbi, akwai hadin guiwa tsakanin Kebbi da Legas, inda Gwamna Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya yanke shawarar jawo daya daga cikin jahohin kasar nan don yin shawara kan hada kai domin kulla huldar kasuwancin amfanin gona.

Baya ga nan Gwamna Bagudu ya kuma tuntubi takwaransa na jihar Legas, Mista Akinwumi Ambode, a lokacin da suka kammala wani taron ganawa na Gwamnonin jihohin kasar nan a Abuja. Domin hada hannu tsakanin jahohin biyu ta hanyar habaka kasuwacin noma, kiwo da ma wasu sauran amfanin gona, wanda zai dawo da arzikin noma da ma arziki kasar nan Nijeriya.

Hakan ya sanya jihohin biyu suka amince da yin hakan domin ci gaban Nijeriya. A ranar laraba 23/3/2016 ne Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da Gwamna Ambode suka sanya wa yarjejeniyar hannu don kasuwancin da suke son su fara, inda suka amince da sa mata suna “LASKEB”.

Wannan yarjejeniyar wata fitila ce aka haska ga sauran jahohin Nijeriya akan maida hankalisu wajen kasuwaci kan amfanin gona da muke nomawa a cikin kasar mu. A kuma Samar da ayyukkan yi ga maras aikin yi, a kuma rage zaman kashe wando ga wasu matasan kasar nan.

Shi dai shirin LASKEB wata hanya ce da aka fito da ita don kara wa kasuwancin kwarin guiwa da kuma kara samar da hanyoyin walwala da jin dadin al’ummar jihohin biyu da kuma farfado da arzikin kasa ta hanyar noma abincin da zai wadatar da mutanen kasar nan baki daya.

Wannan hadin guiwar tsakanin Kebbi da jihar Lagas ta iya samar da shinkafa a babban kasuwar Legas da ake cewa “LAKE RICE”, wanda hakan ci gaba ne sosai da aka samu. Shirin ya taimaka ta fuskancin inganta kasanci da kuma habaka sa.

Haka zalika shirin noma a jihar Kebbi sai nasarori yake ta samu a cikin kwazon da Gwamnan jihar, Sanata Bagudu ya sanya masu zuba hannun jari ga harkar noma domin ba da tasu gudunmuwa. “Labana Rice mills” ta kaddamar da katafaren kamfanin casar shinkafa a cikin garin Birnin-Kebbi a cikin shekara biyu da ta gabata, kuma a cikin wata biyu da suka ga bata Gwamnatin jihar ta Kebbi ta yi kokarin ganin ta bunkasa noma a jihar ta Kebbi. Inda har ta kai hakan ya yi allura wa gwamnatin Nijeriya ta zubura domin inganta sha’anin noman da kuma ganin ta bunkasa harkar noma da kuma farfado da tattalin arzikin kasar. Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kaddamar da wani gagarumin aiki a jihar Kebbi na bude kamfanin sarrafa shinkafa mafi girma a yankin Afrika ta yamma a karamar hukumar Argungu da ke jihar Kebbi mai suna “WACOT RICE Mills”. Inda a cikin jawabin sa na kaddamar da kamfanin na WACOT RICE mills. Mataimakin shugaban kasar ya ce noma da ma’adanai zai kasance daya daga cikin abin da Gwamnatin tarayya za ta ba muhimmaci.

Kimanin shekaru biyu da rabi ke nan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da noman shinkafa a jihar ta Kebbi, duk a cikin tsarin gwamnatin sa na habaka tattalin arzikin kasar ta harkar noma tare da rage dogaro akan man fetur.

Gwamna jihar Kebbi Atiku Bagudu ya ce gwamnatinsa tana gayyatan kungiyoyin kasashen waje a harkan noma da su duba kudirin gwamanatinsa a fannin noma don taimaka wa jihar sa wajen ingatan aikin noma irin na zamani.

Leave a comment