Wata Kotun Kasar Italiya Ta Daure Tsohon  Dan Wasan Kwallon  Kafa Robinho Na tsawon shekaru 9

Wata kotu a kasar Italiya ta daure tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da Manchester city Robinho har na tsawon shekaru tara.

Kotun dai ta ce Robinho mai shekaru 33 dan kasar Brazil yana daya daga cikin gungun mutane da suka yi fyade ga wata mata a birnin Milan a shekarar 2013.

ita ma wata kotu a kasar Afirka ta kudu ta kara wa’adin zama gidan yari ga tsohon zakaran gasar Olympics ta Nakasassu Oscar Pistorius daga shekaru 6 zuwa 13 da wata 5 sakamakon kamashi da laifin kashe budurwarsa.

Tun da fari dai wata kotu ce ta daure Pistorius Shekaru 6 hukuncin da iyalan budurwar tasa da kuma masu gabatar da kara suka ce an yi mishi sassauci sosai.

Leave a comment