Yara Miliyan Biyu Da Rabi Ke Fama  Da Rashin Abinci…. UNICEF

Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF), ya ce, akalla kananan yara sama da miliyan biyu da rabi ne ke fama da rashin abinci mai gina jiki a yankin Arewacin kasar nan.

Wani babban jami’in asusun a Kaduna Idris Bala ne ya bayyana haka yayin wani taro da ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare da kuma asusun na UNICEF suka shirya ga sarakunan gargajiya da kuma shugabannin addinai a arewacin kasar nan da nufin nemo mafita ga matsalar karancin abinci mai gina jiki tsakanin kananan yara.

Babban jami’in na UNICEF, ya ce; Nigeria ce kasa ta biyu a duniya wajen mutuwar yara ‘yan kasa da shekaru biyar, yana mai cewar biyu cikin yara biyar a kasar nan basa samun abinci mai gina jiki.

Ya kuma ce wasu kididdiga da suka tattara sun bayyana cewa akwai kananan yara akalla sama da miliyan goma sha uku da suke fuskantar irin wadannan matsalolin abinci mai gina jiki a kasar nan.

Idris Bala ya kuma ce yankin arewa maso gabashin kasar nan-ne ke kan gaban wajen mutuwar yara kanana sakamakon rashin abinci mai gina jiki wanda ya alakanta hakan da rikicin boko-haram.

Leave a comment