SAUYA SHEKA: Dole Atiku Yabi Ka’idar Jam’iyyar PDP… Walid Jibrin

Jam’iyyar PDP ta bukaci Atiku Abubakar ya bi ka’idojin da jam’iyyar ta gindaya idan ya koma a cikin ta nan da ‘yan kwanaki kadan.

Shugaban Kwamitin amintattu na jam’iyyar Sanata Walid Jibrin ya bayyana haka, a wata zantawa da ya yi da manema labarai.

Jibrin, ya ce masu zawarcin kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP sun karu a kwanakin nan, ya na mai cewa Atiku zai fuskanci ‘yan takara masu yawan gaske.

Ya ce PDP za ta bukaci Atiku a matsayin sa na tsohon mataimakin shugaban kasa ya yi biyayya da kuma bin ka’idojin da jam’iyyar ta shimfida, idan har ya na so su ba shi takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2019.

Sanata Walid Jibrin, ya ce tun daga lokacin da PDP ta ce dan takarar ta daga Arewa zai fito, duk wadanda su ka fito su ka nuna sha’awar su ta tsayawa takara manya ne kuma gogaggu.

Leave a comment