ZAGON KASA: Majalisar Dokokin Kaduna Ta Dakatar Da Wasu ‘Yan Majalisa

 

Rahotanni daga zauren Majalisar dokokin jihar Kadunu Majalisar dokokin jihar Kaduna sun tabbatar da  cewa majalisar ta  dakatar da wasu ‘yan majalisar guda biyu bisa samun da laifin aikata ba dai dai ba.

Yan majalisar da aka dakatar sun fito daga mazabar Zango Kataf da Kaura duk a cikin jihar ta Kaduna.

Rahotanni sun ruwaito cewa majalisar dokokin jihar Kaduna ta dakatar da yan majalisar ta guda biyu daga kudancin Kaduna har sai illa ma sha Allah.

Sai dai har lokacin da muke kammla rubuta wannan rahoton majalisar batayi wani cikakken bayani akan dakatarwarba Sai dai rahotanni sunce dakatarwa tana da nasaba da laifin Yiwa majalisar zagon kasa da aka samesu da shi.

Yan alisar da aka dakatar sune Dakta Bityong Yakubu Nkom, da kuma Hon.  Danladi Angulu Kwasu mai wakiltar karamar hukumar Kaura dukkansu sun kasance daga kudancin jihar.

Leave a comment