Mun Kori Ma’aikatan  Kananan Hukumomi Ne Don Rage Kudadan  Da Muke Kashewa Na Albashi…. Jafaru  Sani

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana  cewa ta sallamai  ma’aikatan kananan hukumominta fiye da 4,000 don rage kudaden da take kashewa a matsayin albashi da kuma bunkasa kudaden gudanar da ayyukan raya kasa.

Gwamnatin  ta kuma  tabbatar da  cewa  matakin ya zama dole don kuwa akasarin ma’aikatan na karbar albashi ne ba tare da aikin komai ba.

Kwamishinan kananan hukumomin jihar, Alhaji Ja’afaru Sani Wanda ya bayyana hakan a wani taron manema Labarai  ya ce gwamnati ta yi wa ma’aikata 3,159 ritaya, yayin da kuma ta kori wasu 8,083 daga aiki


Ya ce su kuma za su samu albashin wata daya kuma a ba su garatuti amma ba za a biya su fensho ba.

A cewarsa matakin zai ba wa kananan hukumomin jihar Kaduna damar gudanar da ayyukan raya kasa da kuma biyan albashi ba tare da an tallafa musu ba.

Duk da bayanan da gwamnati ta sha yi kan fa’idar matakin amma wasu na ganin hakan a matsayin bi-ta-da-kulli ga jama’a kawai, in ji shi.

Alhaji Ja’afaru Sani ya ce idan martabar kananan hukumomi ta dawo kuma talaka ya san cewa karamar hukuma tana yi masa aikin da ya dace, shi kansa yadda zai rika hulda da ita zai sauya

Leave a comment