ZABEN 2019: Dakin Gari Yayi Adabo Da Jam’iyyar PDP, Ya Koma APC

Tsohon gwamnan jihar Kebbi Alhaji  Saidu Usman Nasamu Dakingari ya bar jam’iyar PDP ya koma Jam’iyar APC tare da magoya bayansa. 

Wadanda suka koma jam’iyar ta APC sune kamar haka.

Tsohon Gwamnan Jihar Kebbi Alh. Saidu Usman Dakin Gari da  Tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Ibrahim K. Aliyu da kuma Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi Alh. Garba Rabi’u Musa Kamba

Har ila yau shima Tsohon Shugaban karamar Hukumar Mulkin Birnin Kebbi Alh. Musa Ibrahim Dan illela da Tsohon Shugaban karamar Hukumar Augie Garba Umar Birnin Tudu da Tsohon Shugaban Karamar hukumar Mulkin Kalgo Alhaji Abubakar Kuka duk sun koma APC

Sauran sun hada  Tsohon Dan Majalisar Tarayya Hon. Sani Kalgo  da Tsohon Dan Majalisar Tarayya na Yanzu Zuru Hon. Dan Alkali Durunbun Zuru 

 Itama Tsohowar Yan Yan Majalisar Tarayya ta Yankin Yauri Hon. Halima Hassan Tukur da Alhaji Abubakar Sadik Yalwa Katikan Yauri  sai  Ummaru Maye Yauri da Lawali Na Malam Dakin Gari  Sai Alh. Shehu Ma’azu Zuru  da kuma Alhaji Zayyanu Maigishiri ba’a barsu a baya Ba wajen sauya shekan Ba.

Leave a comment