Yanzu Hakar Kabari A Jihar  Kano Naira Dubu 20 Ne….  Inji Kungiyar Masu Hakar Kabari

Kungiyar masu Hakar makabartu a jihar Kano ta bayyana cewa daga yanzu Hakar kabarin yara ya Koma naira dubu 10 sai na manya naira dubu 20 , inda suka ce yanzu Hakar makarbata ya tashi daga kyauta ya na kudi,

Kungiyar tace Fitar da farashin ya zama wajibi akansu bisa rashin kin biyansu da gwamnan jihar yayi har na tsowon watanni 8, Wanda suka ce suna fuskantar matsalar kuncin rayuwa.

Kungiyar tace sun bawa gwamnatin jihar wa’adin watanni uku idan bata biya su hakkokinsu ba farashin Hakar kabari zai fara aiki kuma babu sani babu sabo akan duk iyalan mamaci dai sun biya kudin Hakar kabari kamin su bari a bizne gawar mamacin.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar ya Samar ya bayyana cewa ya zama musu wajibi da su fara karbar kudin kudin Hakar kabari a jihar Kano domain ta haka ne kawai suna zasu samu damar daukar nauyin iyalansu.

Leave a comment