ZABEN 2019: Babu Abin Da Zai Hana Ni Fitowa Takara…. Shehu ABG 

Tsohon Dan majalisar wakilai wanda ya wakilci  Karamar hukumar Kaduna ta Arewa a majalisar tarayya Abuja, Usman Shehu Bawa (ABG) ya bayar da tabbacin cewa a zaben 2019 mai zuwa zai kara tsayawa takarar kujerar Dan majalisar tarayya,  inda yace babu gudu babu ja da baya wajen ganin Neman kujerar.

Shehu ABG Wanda ya zama Dan majalisar tarayya daga shekarar 2011 zuwa 2015 a inuwar jam’iyyar CPC, ya bayyana cewa duk masu yada jita-jitar cewa ba zai fito takara ba, ba yawunsa sukeyi ba.

ABG Wanda ya bayyana haka a wata zantawa da yayi da manema labarai a Kaduna Jim kadan bayan kammala taron cika shekara goma da kafuwar cibiyar tallafawa masu cutar amosanin mini mai suna ” sickle cell Initiative” Na Hajiya Badiyya Inuwa.

Shehu Bawa, Wanda yanzu mataimakine Na musamman ba shugaban majalisar wakilai ta tarayya Yakubu Dogara, ya kara da cewa a shirye yake da ya kara fitowa takara a zabe mai zuwa, tana mai cewa siyasa da abin ko a mutu ko ayi rai bane, hasalima, yace ya kamata ayi siyasa babu gaba.

Leave a comment