Gwamnatin  Tarayya Ta Kaddamar Da Cibiyar Manoma A Jihar Kaduna

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wata cibiya da manoma za su rika tuntuba domin samun bayanai kan harkokin noma da nufin bunkasa bangaren noma a kasar nan.

Ministan noma da raya karkara Audu Ogbeh ne ya bayyana haka ga manema labarai yayin wata ziyara a cibiyar nazarin noma da ke Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zari’a a jihar Kaduna.

Ya ce cibiyar za ta taimaka gaya wajen tallafawa manoma ta bangarori da dama a don haka ya bukace manomar da su rika tuntubar cibiyar domin nemo mafita kan abubuwan da suka shige musu duhu.

Ministan ya kuma ce nan ba da dadewa ba gwamnati za ta yi hadin gwiwa da cibiyar nazarin noma da ke Jami’ar Ahmadu Bello a Zari’a domin ta rika horas da jami’an noma da ke aiki da ma’aikatar noma da raya karkara.

Da ya ke gabatar da jawabi shugaban cibiyar nazarin noma a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zari’a Farfesa Muhammad Khalid Othman, ya yaba da kokarin da ministan ke yi wajen yin hadin gwiwa da cibiyar domin bunkasa bangaren noma a kasar nan

Leave a comment