ZABEN 2019: Buhari Yana Da Koshin Lafiyar Sake Tsayawa Takara – Adesina

Fadar shugaban kasa ta ce, shugaba Muhammad Buhari na da koshin lafiyar da zai iya sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2019.

Mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar yada labarai Femi Adeshina ya bayyana haka a wata zantawa da da ya yi da manema labarai a Abuja.

Adesina, ya ce lafiyar shugaba Buhari ta yanzu ta fi inganci fiye da lafiyar sa a shekara ta 2015.

Ya ce duk da dai shugaba Buhari bai yanke shawarar sake tsayawa takara ba, amma lafiyar sa ba za ta kawo ma sa cikas ba, saboda yadda ta inganta tun bayan dawowar sa daga jinyar da ya yi a London.

Femi Adesina, ya kuma musanta rade-radin da ke cewa shugaba Buhari ya nada ministan sufuri Rotimi Amaechi a matsayin daraktan yakin neman zaben sa a shekara ta 2019.

Leave a comment