Kwankwaso Ya Dage Ziyararsa Zuwa Jihar Kano

Tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya dage ziyarar da yayi shirin kawo wa  jihar Kano a ranar 30 ga wannan watan.

Da ya ke jawabi, tsohon Sakataren gwamnatin jihar Kano Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, ya bayyana cewa sanata Kwankwaso ya janye kawo ziyarar tasa ne sakamakon tun tubar wadanda abin ya shafa.

Sanata Kwankwaso ya kuma kara da cewa a dage kawo ziyarar tasa ne don gujewa samun hargitsi da tashin hankali yayin ziyarar, biyo bayan shawarwari daga gurare daban-daban.

Sanata Kwankwaso ya kuma baiwa Al’ummar Jihar Kano Hakurin dage ziyarar tasa yana mai cewa hakan ya zama dole don kare rayukan al’umma da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Leave a comment