‘Yan Siyasa Keda Hannu Wajen Kashe-Kashen Fulani Da Manoma– Bafarawa

Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana cewa yan siyasa ne ke da hannu wajen kashe-kashen da ake samu a fadin kasar nan wadanda ake danganta su da Fulani Makiyaya.

A wata tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP da ya gudana a jihar Sokoto, inda ya tabbatar da cewa kashe-kashen siyasa ce zalla.

Bafarawa ya kuma kara da cewa wasu yan siyasa marasa kishin kasa ne ke amfani da mutane wajen cimma burin su na siyasa ko da kuwa hakan ka iya salwantar da rayukan jama’a.

Alhaji Attahiru ya kuma shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rika amfani da shawarwarin da yan Najeriya ke bashi, batare da la’akari da wanda ya bada shawarar ko jam’iyyar sa ba.

Ya kuma kara da cewa abin da yan Najeriya ke bukata shine ingantaccen shugaba ko da kuwa daga wace jam’iyya yake.

Leave a comment