Gwamnatin jihar Katsina Zata Fara Ciyar Da Dalibai Abinci A Wannan Watan

Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da tabbacin cewa za ta fara ciyar da dalibai ‘Yan firamare abinci a cikin wannan watan da muke ciki.
Mai bawa Gwamnan shawara akan harkar ilimin ‘ya’ya Mata Hajiya Binta Abba Umar, ita ce ta bayyana hakan inda tace gwamnati tafara ba jami’anta kudade domin fara shirin.
Hajiya Binta Abba Umar tayi kira ga iyaye da Malamai da kuma sauran al’umma da su sa ido don ganin shirin ya tabbata.
Hajiya Binta ta yi kira da mata da su dunga amsar katin zabe domin zabar shuwagabanni na gari.
Daga karshe ta yi kira da mata da su dunga shiga sha’anin siyasa domin a rika damawa da su a dukkanin bangaorin gwamnati

Leave a comment