Wata Budurwa Ta Bankawa Kanta Wuta A Kan Saurayi

Soyayya rayuwa; Wani mummunan lamari ya faru a wani gida da ke titin Salihi a Unguwar Kofar Fada da ke cikin karamar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa, inda wata budurwa ta hallaka kanta saboda saurayi.
Ita dai wannan budurwa mai suna Hafsat Aminu mai shekaru 19 ta dauki wannan mummunan mataki ne a kanta biyo bayan kokarin rabata da saurayinta da aka yi, inda ta daddaki kalanzir, ta yi wanka da shi, sa’annan ta banka wa kanta wuta.
Majiyarmu ta samu labarin cewa iyayen Hafsat ba sa tare da juna, inda tun kimanin shekaru 17 da suka gabata ne mahaifiyar Hafsa da mahaifinta suka rabu, amma tana zama tare da mahaifiyarta da mijinta na yanzu, Malam Abubakar Ahmed Gumel.
A lokacin da Abubakar Gumel da Malama Abu mahafiyar Hafsa suka samu labarin abin da ya faru nan da nan suka garzaya da ita cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Birnin Kudu, da abin ya ci tura sai suka garzaya da ita zuwa babban asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, inda ta cika a can.
Da majiyarmu ta tattauna da saurayinta, Haruna Ibrahim mai sana’ar Tela, ta tabbatar da alakarsa da Hafsa,inda ya ce kwata-kwata ba su wuce watanni 8 ba, amma sun shaku matuka.
A cewarsa, bai ji cewa saboda shi Hafsa ta kashe kanta, ya fi tunanin aljanu ne, saboda dama ya ce tana da aljanu, don koda ta dawo cikin hayyacinta ta ga abin da ya faru, sai da ta yi mamaki, a cewarsa.
A nasa bayanin, mahafin Hafsa, Malam Aminu Yakubu, malami a sakandaren Arabiyya ta Birnin Kudu ya tabbatar da mutuwar ‘yar tasa, amma kuma rabonsa da ita sama da shekara 17, tun lokacin da aurensu ya mutu da mahaifiyarta.
Malam Aminu ya ce bana Hafsa ta kammala sakandare, kuma yanzu haka sunanta yana cikin jerin daliban da aka dauka domin yin karatun fannin lafiya a makarantar Ungozoma ta Birnin Kudu, sai ya ce kwananta ne ya kare kuma ba ya da wani abu da zai fada illa Allah Ya jikanta Ya yi mata rahama.
Sai dai ya musanta batun da ake yadawa na cewa wai za a yi mata auren dole ne:
“Yaron da ake cewa yana soyayya da ita dan uwana ne ba ya da wata matsala kuma babu batun maganar auren dole, kamar yadda ake bazawa wai za a yi mata shi ne ya sa ta kone kanta. saboda haka batun a ce wai auren dole za a yi mata ta hallaka kanta ba gaskiya ba ne.”

Leave a comment