ZABEN2019: Ni Zan Jagoranci Kada Gwamnan jigawa — Sanata Ubale Shitu

“Ni zan jagoranci Kada gwamnan jihar jigawa a zaben 2019 insha Allah, inji Dan majalisar dattawa mai wakiltar Arewacin jihar jigawa a majalisar dattijan Nijeriya Sanata Mohammed Ubale Shitu.
Sanata Mohammed Ubale Shitu, ya bayyana taikacinsa dangane da yadda gwamnan ya mayar da jihar jigawa koma baya wajen kawo ci gaba inda yace babu shakka al’ummar jihar jigawa zasu Kada gwamnan a zabe mai zuwa.
Sanata Mohammed Ubale Shitu, ya bayyana haka ne a wata zantawa da yayi da wakilinmu a jihar Katsina Jim kadan bayan kammala taron kungiyar sanatocin Arewa Wanda aka gudanar da shi a jihar Katsina.
” Lokaci yayi da al’ummar kasar nan bama jihar jigawa ba kawai su natsu wajen zaben shugabanninsu a zabe mai bisa la’akari da cewa a zaben shekarar 2015 anyi zaben mutum dare ba’ayi zabe bisa cancanta ba. Saboda haka wannan karon babu SAK cancanta za’ayi” inji Sanata Shitu.
Dan majalisar yayi Allah wadai da yadda gwamnan jihar jigawa Abubakar Badaru, yake jagoranci jihar, inda yace al’ummar jihar jigawa sunyi zaben tumun dare wajen zaben gwamna Badaru.
Akan hakan, Dan majalisar ya kara jaddada kudurinsa na tabbatar da cewa ya jagoranci al’ummar jihar jigawa wajen Kada gwamnan Badaru a zaben 2019 mai zuwa, yana mai cewa” ina mai tabbatar muku da cewa insha Allah nine zan jagoranci Kada gwamna Badaru a zabe mai zuwa saboda babu abin da ya tabuka illa yawa kasashe kasashe yana bunkasa harkar kasuwancinsa.
Daga karshe, Dan majalisar, ya bukaci daukacin al’ummar kasar nan musamman na Arewacin kasar nan da su kaucewa zaben jam’iyya inda yace su zabi mutumin kirki Wanda hakan shine zai taimaka wajen kawo ci gaban yankin Baki daya.

Leave a comment