Gwamnatin Jihar Benue Ta Janye Aniyar Gwanjon Shanun Fulani

Gwamnatin Jihar Benue ta janye aniyarta, na yin gwanjon wasu shanun fulani makiyaya da ta kame bisa laifin karya dokar hana kiwo da ta kafa a jihar.
Hakan ya biyo bayan tattaunawar da gwamnan jihar Samuel Ortom ya yi, da shugabanin kungiyar , inda ya amince da mika musu shanun.
Ubbi Haruna, shugaban kungiyar ta Miyyati Allah ya bayyana farin cikin sa tareda yi kira zuwa magoya bayan su don ganin sun bayar da hadin kai.
Rahotanni sun ruwaito cewa kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International na cewa akalla mutane 168 ne suka rasa rayukansu a jihar Benue daga watan janairu mai zuwa.

Leave a comment