Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sako Mahaifiyar Na Goggo Shema

Rahotanni sun ruwaito cewa ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da Hajiya Diya, mahaifiyar dan kasuwar nan dake da gidajen sayar da man fetur na “Shema Petroleum” ta kubuta daga hannun masu garkuwa da ita.
A satin da ya gabata ne barayin sun je gidan matar dake Dutsin-ma inda suka yi awon gaba da ita bayan sun yi harbe- harbe.
Majiyarmu ta rawaito cewa barayin da farko sun nemi a basu naira miliyan dari biyu a matsayin kudin fansa kamin su sako dattijuwar mai shekaru 82.
Sai dai a yanzun Katsina Post ba ta da tabbacin an biya kudi kamin fitowar tata a hannun yan bindigar.
Kamar dai yadda muka samu, daya daga cikin yayan ta Nagarhi Abubakar ya bayyana cewa an sako ta ne a cikin koshin lafiya ba tare da sun cutar da ita ba.

Leave a comment