ZABEN 2019: Zamu Fito Da Dan Takarar Da Yafi Buhari Cancanta – Inji PDP

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ta shirya tsaf, domin kwace kujerar mulki daga hannun jam’iyyar APC ta hanyar fito da dan takarar da ya fi shugaba Buhari nagarta a zaben 2019 Mai zuwa,
Tsohon Ministan sufuri Chief Ebenezer Babatope ya bayyana haka, yayin wata zantawa da yay i da manema labarai a Abuja.

Ya ce a zabe mai zuwa, PDP za ta natsu ta yi tunani sannan ta fitar da dan takarar da zai iya kawo wa Nijeriya cigaban da ya fi na gwamnatin shugaba Buhari.
Babatope ya kara da cewa, jam’iyyar PDP ba za ta yi la’akari da cewa ko babban dan siyasa ne ko karami ba, cancanta za su bi su fitar da wanda zai yi wa talakawa aiki, kuma za su bada dama ga kowa ba tare da nuna fifiko ba.

A cewar sa, PDP ba ta girgiza da jin sake tsayawar shugaba Buhari takara baba, domin ya na da yan cin yin hakan, amma tabbas za su tabbatar sun tsaida wanda zai kada shugaba Buhari a zaben shekara ta 2019.

Leave a comment