CBN Ya Saki Dala Miliyan 100 A Kasuwar Musayar Kudadan Kasashen Waje

Babban bankin Nijeriya CBN, ya bayyana cewa ya saki dala miliyan 100 a kasuwar musayar kudaden kasashen waje.
A cewar bankin na CBN hakan na zuwa ne awanni 24 bayan tunkudo dala miliyan 210 a ranar Larabar da ta gabata.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun bankin Isaac Okorafor.
Isaac Okorafor ta cikin sanarwar dai ya kuma ce an tunkudo kudin musayar ne domin saukakawa al’ummar kasar nan da ke fita ketare domin gudanar da wasu muhimman bukatun da suka wajaba a kansu musamman maniyyatan aikin Hajji bana.
Bankin na CBN a sanarwar ya kara da cewa zai ci gaba da tunkudo dala kasuwar musaya domin dakile karancinsa. Sai dai ya ce zai sanya ido sosai domin tabbatar da cewa wadanda suka cancanta ne kawai suka amfana

Leave a comment