Jaridar Blueprint Ta Karrama Shehu Sani

A bisa jajircewa wajen fadin gaskiya da tallafawa al’umma, jaridar Blueprint Ta Karrama Sanata Shehu Sani da lambar yabo bisa kokarinsa na kawo ci gaban kasar nan baki daya.

Sanata Shehu Sani, Wanda shine Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar tsakiyar jihar kaduna a majalisar dattawa , ya godewa jaridar bisa sanya shi cikin muhimman manyan mutane da jaridar ta Karrama.

An gudanar da bikin Karramawar ne a dakin taro na Otel din Rockview da ke Abuja a yau talata .

Da yake jawabi bayan karbar lambar yabon Sanata Shehu Sani , ya kara jaddada goyon bayansa akan kalaman shugaban kasa muhammad Buhari na cewa a zaben 2019 al’ummar kasar nan su zabi mutane bisa cancanta inda yace yana goyon bayan kalaman shugaba kasa.

Shehu Sani , yace idan al’ummar kasar nan sukayi cancanta babu shakka za’a samu sauyin batagarin shugabanni a shekarar 2019 mai zuwa.

Mutanan da jaridar ta Karrama sun hada da: gwamnan jihar Gombe da na katsina da Yobe da Kano da kuma gwamnan babban bankin Nijeriya.

Sauran sun hada da , Ministan Sufuri Rotimi Ameachi da Sanata Shehu Sani da Tukur Yusuf Buratai da shugaban hukumar Aikin hajji na kasa Abdullah Mukhtar da dai sauransu.

Leave a comment