Zamuyi Hadaka Da Gwamnatin Jihar Kaduna Wajen Samar Da Guraban Ayyukan Yi … Kamfanin Bizi Mobile

A bisa kokarin da gwamnatin bayyana Nijeriya ring take yi kara bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasa musaman na samar da guraben ayyukan dogaro ga matasa musamman a bangaran hada-hadar kudade wajen kasuwanci wanda hakan ya sanya babban bankin Nijeriya CBN ya samar da hanyoyin tallafawa harkar ci gaban hada -hadar kasuwancin domin amfanar al’ummar kasar nan.

Masana tattalin arzikin kasa sun bayyana yunkurin babban bankin Nijeriya CBN ya fito da shi na fitar da kudade cikin sauki ga ‘yan kasa, da kuma hadin gwiwar da gwamnatin jihar Kaduna tayi da Kamfanin Bizi Mobile, Kamfanin dake taimakawa ‘yan kasa wajen saukin fitar da kudade, ya taimaka matuka wajen kara samar da ayyukan yi ga dimbin matasan Nijeriya.

Shugaban Kamfanin Bizi Mobile na kasa Alhaji Aminu Bizi, shine ya bayyana hakan, lokacin da yake zantawa da manema Labarai jim kadan bayan kammala wani taro na horaswa da babban bankin Nijeriya ya shirya da had in gwiwar kamfanin Bizi Mobile domin fadakar da jama’a hanya mafi sauki wajen gudanar da harkar shige da fice na kudaden su, wanda ya gudana a Seventeen Hotel Kaduna.

Aminu Bizi ya cigaba da cewar, tuni kamfanin shi ya horas da ma’aikatan shi har sama da 12,000 wadanda suma da akwai wasu ma’aikatan a karkashin su a fadin kasa baki daya.
Dangane da shigowar gwamnatin jihar Kaduna cikin tsarin ta hanyar ma’aikatar mata ta jihar kuwa, Shugaban Kamfanin na Bizi yace yana yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna El Rufai, bisa jajircewar su wajen inganta rayuwar matasa, domin da kudin ka naira 1000 kana iya zama Muloniya a tsarin Bizi Mobile cikin sauki, saboda haka wannan wata dama ce ga dukkanin masu kananan sana’o’i tun daga kan masu sayar da shayi, da masu a daidaita sahu, da ‘yanzu acaba da sauran ‘yan Boko marasa ayyukan yi, da su shigo tsarin Bizi Mobile tun fita daga talaucin rayuwa.

Mahalarta taron da dama wadanda aka zanta da su, sun yaba gami da jinjinawa ga kamfanin Bizi Mobile kan kokarin da yake na kawar da talauci da kuma samar da rayuwa ingantacciya ga matasan Nijeriya.

Leave a comment