‘Yan Fanshon Jaridar New Nigeria Newspaper 180 Suka Rasu Cikin Shekaru 6

Kungiyar ‘yan Fansho na kamfanin Wallafa jaridar New Nigeria Newspaper da Gaskiya Tafi Kwabo ta bayyana cewa ‘yan fansho guda 180 ne suka rasa ransu a cikin shekaru shida da suka gabata bisa tunani da alhinin rashin biyansu kudaden su na fansho da sauran hakkokinsu da gwamnatin tarayya ta gaza biyansu.

Bayanin alkaluman ya fito ne daga bakin Sakataren Kungiyar Mista Albert Bosa Iweka, inda yace ‘yan fansho na kamfanin Jaridar New Nigeria Newspaper suna bin gwamnatin tarayya kudin fansho na shekaru goma sha biyar (15) yana mai cewa rayuwar su tana cikin mawuyacin hali , lamarin da ya kaiga suna rasa rayukan mambobin su.

Mista Bosa , ya kara da cewa gwamnatin Buhari ta ware naira biliyan 2 domin biyansu hakkokinsu tun a shekarar 2017 Amma har yanzu babu labari.

Kungiyar ta bayyana gamsuwar ta Dangane da kokarin shugaban kasa muhammad Buhari, na bayar da umarnin a biya su hakkokinsu Amma wasu marasa kishin al’umma sun dakile komai.

Akan Mista Albert Bosa, ya nuna rashin jin dadin su akan irin matakin da ma’aikatar Kudi ta kasa ta gaza biyansu kudaden su na fansho naira biliyan 2 duk kuwa umarnin shugaban kasa da umarnin kotu data ce a biyasu hakkokinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa a watan Oktobar shekarar 2013 wata babbar kotu ta yanke hukuncin cewa a gwamnatin tarayya da Kamfanin Jaridar New Nigeria Newspaper su gaggauta biyansu kudaden su na fansho da sauran hakkokinsu Amma har yanzu babu Labari.

Leave a comment