Za’a Tilastawa Ma’aikatan Gwamnati Amfani Da Jirgin NIGERIAN AIR Da Zarar An Kaddamar Da Shi

A kokarinta na ganin an bunkasa harkokin Sufurin Jirgin saman kasar
nan gwamnatin tarayya ta sanar da fara wani yunkuri na tilastawa
ma’aikatanta tafiye-tafiye ta sabon kamfanin da aka kaddamar na
kasa Nigeria Air.
Karamin Ministan Sufurin Jiragen sama Hadi Sirika ya ce gwamnatin
tarayya ganin Majalisun tarayya sun yi dokar da za ta tilasta hakan
don ganin komai ya tafi yadda aka tsara.
Ministan ya bayyana cewa ba didai ba ne yadda wasu ke cece-ku-ce
da takaddama dangane da inganci da kuma ‘yancin sunan kamfanin,
kamar yadda wasu ke muhawara a kai a shafukan zumunta na
zamani.
Ya kuma kara da cewa batun yarjejeniyar da gwamnatin ta kulla da
‘yan kasuwa abu ne mai kyau da zai haifar da ‘da mai ido cikin
kankanin lokaci matukar harkokin suka kankama.

Leave a comment