Dalilin Da Yasa Nayi Lalata Da ‘Yata… Wani Magidanci

Wani matashi mai shekaru 30 Basiru Audu, ya fada Hannun hukumar tsaro ta yan-sanda bisa zargin da yin lalata da yar cikinsa mai shekaru 6.
Lamarin ya afku a London street cikin garin Minna jihar Niger, a
lokacin da yarinyar ta shiga cikin gidan makwabtansu tana tafiya a
karkace, inda suka tambayi mike damunta, sai ta ce babanta ne ya
sa mata wani abu cikin dare a farjinta.
A lokacin da Yan-sandan jihar ta Niger suka cika hannu da shi sai
ya kada baki ya ce, mai dakinsa ce ta tafi garinsu na Daura jihar
Katsina, shi kuma ya matsu da sha’awar yin jima’i, kawai sai ya
lallaba dakin yarinya ya kwanta da ita, inda shi da kansa ya kira
cewa wannan abin kunyar dame yai kama, kamar yadda majiyarmu
ta Northern City News ta rawaito mana.
” Na zagi matata a lokacin da nake cikin matsananciyar sha’awar
yin kwanciyar aure da ita, ta yi tafiya mai nisa can zuwa garinmu na
Daura, hakan ne ya jawo man kwamciya da ‘yata ,wannan abin
kunya da me yai kama? ” inji mai laifin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Yan-sandan jihar Muhammad
Abubakar, ya ce wanda ake zargin bai musanta aikata laifin nasa
ba, sannan ya nuna ladamarsa ta aikata hakan.
Sannan ya kara da cewa alamun tashin duniya ne kawai ya zo da
har uba zai iya lalata da yar cikinsa mai kuma kananan shekarun da
ba ta wuce shekaru 6 ba

Leave a comment