2019: Idan Mataimakina Ya Tafi Majalisar Dattawa, Zan Zama Maraya…El-Rufai

A dai dai lokacin da Mataimakin gwamnan jihar Kaduna Barnabas Bala Bantex, ya bayyana aniyarsa na tsayawa takarar kujerar dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar kudancin Jihar Kaduna a zaben 2019 mai zuwa,Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa idan Mataimakin gwamnan ya barshi ya tafi majalisar dattawa zai koma Maraya.

Gwamna El-Rufai , ya wanda yake Bayani cikin alhini ya ce shakuwarsu da Mataimakin gwamnan ya wuce ta siyasa,yana mai cewa idan Mataimakin Ya barshi babu shakka zai zama Maraya saboda bai San wanda zai maye makwafinsaba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema Labarai kai tsaye a daukacin gidajen Rediyon da suke jihar Kaduna.

Akan hakan, Gwamnan yace kofa a Bude take ga masu Neman kujerar Mataimakin gwamnan inda yace yanzu zai fara laluben wanda zai masa Mataimakin gwamnan a zaben 2019 mai zuwa.

El-Rufai, yace takarar Mataimakinsa kujerar dan majalisar Dattawa shugaba Muhammadu Buhari shi ya fara amincewa da bukatarsa.

Gwamna El Rufai, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ya fara amincewa da takarar Mataimakin gwamnan lokacin da Mataimakin gwamnan ya bayyana aniyarsa na tsayawa takarar kujerar dan majalisar dattawa ga shugaban kasa, acewar gwamnan tun watanni shida da suka gabata shugaban kasa ya Amince Da kudirin Mataimakin gwamnan.

El-Rufai ya ci gaba da cewa “kamar yadda nace kimanin watanni shida zuwa bakwai Mataimakin Gwamna na ya fadawa shugaba Buhari cewa zai ba zai tsaya takarar Mataimakin Gwamna a shekarar 2019 ba , za tsaya takarar kujerar dan majalisar dattawa ne saboda hakan zai bashi damar wakiltar jama’arsa yadda ya kamata. Nan take shugaba Buhari Ya Amince Da kudirin Bantex inda yace majalisar dattawa tana bukatar mutane irin Bantex” inji shi.

Leave a comment